in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gada ta biyu ta kogin Beilun ta kara azama kan yin ciniki tsakanin kasa da kasa
2019-04-17 13:45:31 cri

Birnin Dongxing da ke jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta ta kasar Sin , birni ne daya tak a nan kasar Sin da ke hada kungiyar kawancen kasashen gabas da kudancin Asiya wato ASEAN a teku da kasa. Akwai wani kogi a tsakaninsa da birnin Móng Cái da ke arewacin kasar Viet Nam. An fara aiki da gada ta biyu ta kogin Beilun a watan jiya a hukumance, wadda ta hada wadannan birane 2 baki daya, inda kuma take sassauta matsin lambar kwastam a gada ta farko ta kogin Beilun tare da kyautata sufurin tasoshin bincike. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China