in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Kenneth a arewacin Mozambique ya kai 38
2019-04-30 10:21:14 cri

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Kenneth a lardin Cabo Delgado na arewacin Mozambique ya karu zuwa 38, yayin da wasu 39 kuma suka jikkata.

Wata sanarwa da cibiyar lura da annoba ta kasar ta fitar, ta ce kusan gidaje 35,000 ne wani bangare nasu ya lalace ko kuma suka lalace baki daya da gonaki da fadinsu ya kai kadada 31,256, tun bayan da mahaukaciyar guguwar ta zo da mamakon ruwan sama da guguwa a ranar 25 ga watan nan.

An kafa cibiyoyin 30 na tsugunar da jama'a a fadin lardin, wadanda suka bada mafaka ga mutane sama da 2,000.

Saviano Abreu, shugaban ofishin kula da agajin jin kai na MDD a kasar, ya shaidawa manema labarai cewa, har yanzu rashin kyawun yanayi a lardin Cabo Delgado na tarnaki ga aikin kai kayayyakin agaji yankunan da guguwar ta shafa.

Hukumar kula da yanayi ta kasar ta ce har yanzu akwai barazanar mamakon ruwan sama a lardin.

Mahaukaciyar guguwar Kenneth ta aukawa kasar ne makonni 6 bayan mahaukaciyar guguwar Idai ta auka yankin tsakiyar kasar, inda ta haifar da guguwa mai tsanani da ambaliya, tare da sanadin mutuwar mutane sama da 600. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China