in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar masu aikin ceto na kasar Sin sun bada gudunmuwar kayayyakin rage radadin iftila'i ga kasar Mozambique da guguwar Idai ta aukawa
2019-04-03 10:45:08 cri
Tawagar masu aikin ceto na kasar Sin, sun bada gudunmuwar kayakin rage radadin iftila'i ga hukumomin lafiya na kasar Mozambique, jiya Talata a Beira, babban birnin Lardin Sofala da mahaukaciyar guguwar Idai ta fi daidaitawa.

Kayayyakin da darajarsu ta kai dala dubu 700 sun hada da; kayayyakin ceto da na asibiti da magunguna da gadajen tafi da gidanka da kuma tantuna.

Da yake godewa kasar Sin, Daraktan sashen aikin agajin kiwon lafiya na ma'aikatar lafiya ta kasar Ussene Issa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, gudunmuwar ta kasar Sin, za ta ragewa ma'aikatar lafiyar nauyin dake kanta na magance bukatun gaggawa da ake da su yanzu.

Ya ce ba gudunmuwa da suka karba jiya kadai kasar Sin ta bayar ba, domin ta shiga ayyukan kula da wadanda mahaukaciyar guguwar ta rutsa da su da rabon abinci da ruwa. Ya kara da cewa, abun da suka samu daga kasar Sin shi ne goyon baya da karfin gwiwar da suke bukata.

Kididdigar da aka fitar a hukumance, ta nuna cewa, mahaukaciyar guguwar Idai da ta aukawa yankin tsakiyar Mozambique a ranar 14 ga watan Maris da daddadare, ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 518 tare da lalata gidaje 59,910 da hanyoyin ruwa da na tsaftar muhalli. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China