Kakakin majalisar Stephane Dujarric, ya ce daga cikin cibiyoyin 11 da aka kafa, guda 9 na aiki, ciki har da na yankin Beira da guguwar ta fi shafa.
Ya ce a gobe Laraba ne za a fara riga kafin cutar kwalara. Ya ce cikin sa'o'i 24 da suka wuce, an samu rahoton mutane 258 sun kamu da cutar. Kuma akwai hadarin yaduwar cutar, la'akari da mutane 276 da suka kamu da ita a yankunan da iftila'in ya aukawa.
Ya ce majalisar kula da tattalin arziki da zamantakewa ta MDD, za ta gudanar da taron na musammam game da kai dauki kasashen Mozambique da Malawi da Zimbabwe, da iftila'in ya aukawa. (Fa'iza Mustapha)