A cikin kwanakin biyu, tawagar bada taimako ta kasar Sin ta tura rukunoni uku don samar da gudummawa ga birnin Beira na jihar, da matsugunar masu fama da bala'in, da yankin kogin Buzi. An ce, tawagar ta bada aikin jinya ga masu fama da bala'in fiye da 500 tare da bayar da magunguna iri iri ga masu fama da bala'in fiye da 400.
A yankin kogin Buzi, rukunin tawagar ya yi bincike kan yanayin gabar kogin don sanin yanayin kogin da hanyar tafiyar kogin da yanayin kauyukan dake gabar kogin, ta hakan za a tsara shirin bada taimako na nan gaba. (Zainab)