Filipe Nyusi ya bayyana haka ne jiya da yamma a Beira na lardin Sofala, bayan ya tattauna da kungiyoyin agaji daban-daban, da kuma yin shiru na wani lokaci domin girmama wadanda iftil'ain ya shafa.
Ya ce agajin zai kasance karkashin bangarori 5 da suka hada da; tallafin abinci da magunguna da matsuguni da ruwa da kuma tsaftar muhalli.
A cewar shugaban kasar, dawowar harkokin rayuwa a yankunan da iftila'in ya shafa na bukatar sake fasalin agajin da ake bukata, wanda zai mayar da hankali kan ayyukan gona da kayayyakin gini da sauransu.
Shugaba Nyusi ya ce, gwamnati za ta raba kayayyakin aikin gona a yankunan, yana mai alkawarin gaggauta sake gina su domin rayuwa ta koma kamar yadda take a baya.
Ya kuma sanar da matakan magance tasirin rayuwa kan iyalan da iftila'in ya shafa, ta hanyar rage kudin da ake biya a cibiyoyin kiwon lafiya da sufuri da makamashi. (Fa'iza Mustapha)