Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Libya, ya bayyana fargabar cewa, ciyar da fararen hula da suka makale saboda yaki a sassan birnin Tripoli, na kara zama matsala mai tsanani, duk da kiran da ake yi na kare fararen hula daga hare-haren.
Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce shirin ya damu da yadda isar abinci ga fararen hula da 'yan gudun hijira da masu kaura dake yankunan da ake rikici ke kara zama babbar barazana.
Ya ce suna ci gaba da kira da a ba jami'an agaji damar kai dauki ga bukatun al'umman da fadan ya shafa, ba tare da wani sharadi ba.
Da yake bada misali daga rahotannin kungiyoyin lafiya, ya ce wani yaro da hare-haren ta sama ya rutsa da shi ya mutu. Ya ce tun bayan barkewar rikicin a farkon watan nan, an tabbatar da jimilar fararen hula 96 da hare-haren suka shafa, ciki har da 22 da suka mutu. (Fa'iza Mustapha)