in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Libya ta yi kashedi game da aniyar sojoji ta karbe babban birnin kasar
2019-04-04 10:05:08 cri
Gwamnatin kasar Libya mai samun goyon bayan MDD, ta yi kashedi game da illar aniyar sojojin kasar masu sansani a gabashi, ta karbe babban birnin kasar Tripoli.

Gwamnatin mai helkwata a Tripoli, ta ce duk wani mataki na soji ba zai warware matsalar da kasa ke ciki ba, sai ma dai tsunduma 'yan kasar cikin wani mawuyacin hali.

Da safiyar jiya Laraba ne dai mai magana da yawon rundunar sojojin yankin gabashi Ahmad al-Mismari, ya shaidawa wata kafar talabijin ta kasar cewa, sojoji na shirin nausawa yammacin kasar zuwa birnin Tripoli, a wani mataki na yunkurin amshe ikon yankin.

Kalaman na Al-Mismari, na zuwa ne gabanin taron masu ruwa da tsaki da MDD ke fatan kira, domin tattauna batutuwan da suka jibanci kasar ta Libya, da nufin kawo karshen sabanin siyasa dake haifar da zaman doya da man ja.

Yanzu haka dai Libya na da gwamnatoci guda biyu dake raba iko a yammaci da gabashin kasar, kuma dukkanin sassan biyu na ikiranin gudanar da halastacciyar gwamnati. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China