in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mutanen da suka mutu a Libya ya kai 21 a rikicin Tripoli
2019-04-08 09:13:00 cri
An samu karuwar adadin mutanen da suka mutu a wani tashin hankali da ya barke a kusa da Tripoli babban birnin kasar Libya tsakanin dakarun dake samun amincewar MDD da mayakan dake da helkwatarta a gabashin Libya, a halin yanzu adadin wadanda suka mutu ya kai 21, a cewar ma'aikatar lafiyar kasar.

"Bisa bayanan babbar hukumar gudanarwar ma'aikatar lafiyar kasa, yawan wadanda aka hallaka a tashin hankalin sun kai 21 sannan wasu 27 kuma sun jikkata," inji ma'aikatar lafiyar.

Dakarun sojojin, wadanda Khalifa Haftar ke jagoranta, sun kaddamar da harin soji ne a ranar Alhamis domin kwace ikon yankunan yammacin Libya, musamman babban birnin kasar Tripoli inda gwamnatin dake samun goyon bayan MDD ke da helkwatarta.

Tun da farko a ranar Lahadi, mai magana da yawun dakarun gwamnatin ya sanar da cewa, tuni sojojin gwamnatin suka mayar da martani kan harin da mayakan 'yan adawar suka kaddamar.

Kasar Libya ta fada rikicin shugabanci da tashe tashen hankula da rashin tsaro ne, tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Gaddafi a shekarar 2011.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China