in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Libya ya bukaci dukkan bangarorin dake rikici a kasar su shiga a dama da su wajen samar da mafita ga rikicin kasar
2019-03-20 10:23:40 cri
Firaministan Libya da MDD ke marawa baya Fayez Serraj, ya yi kira ga dukkan bangarorin kasar dake rikici, su shiga a dama da su wajen samar da mafita ga rikicin siyasar kasar.

Fayez Serraj, ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da Kwamnadan rundunar kawance tsakanin Afrika da Amurka (AFRICOM) Thomas Waldhauser, da kuma Jakadan Amurka a Libya Peter Bodde.

Wata sanarwar da ofishin yada labarai na Firaministan ya fitar, ta ruwaito Fayez Serraj ya yi bayani kan kokarin da yake na cimma yarjejeniya a kasar, ta hanyar ganawa da dukkan muhamman jam'iyyun kasar.

Ya kuma bayyana bukatar kafa gwamnatin farar hula a Libya, tare da hade kan rundunar sojin kasar.

Bangarorin biyu sun amince da su mara baya ga shirin manzon musamam na MDD Ghassan Salame na karfafa tsarin demokradiyyar kasar, ta hanyar gudanar da zabukan majalisun dokoki da na shugaban kasa, wanda zai bada damar gudanar da babban taron kasa.

Sun kuma jadadda cewa, babu wani matakin soji da zai shawo kan rikicin da Libya ke ciki a yanzu. (Fa'iza Musatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China