in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta zurfafa gyare-gyare da take yi a gida da kara bude kofa ga waje domin biyan bukatun kanta
2019-04-29 20:11:13 cri

Yau Litinin Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, kasar Sin ce da kanta ta tsai da kudurin zurfafa gyare-gyare da take yi a gida da kara bude kofa ga waje, a kokarin biyan bukatun kanta na raya kasa. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufarta bisa matakai, ajanda da kuma taswirar da ta tsara.

Geng Shuang ya fadi haka ne yayin da yake amsa tambayar manema labaru dangane da rahotanni da wasu kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya suke watsawa cewa, kila kasar Sin ta sanar da daukar wasu manyan matakan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje ne domin biyan bukatun kasar Amurka.

Geng Shuang ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta hada kai da aminanta wadanda ke da buri iri daya wajen kara samun sakamako ta fuskar aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", za kuma ta inganta hadin gwiwa da kasashen duniya domin samun moriyar juna da nasara tare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China