James Laurenceson, mataimakin darektan cibiyar nazarin huldar dake tsakanin Australia da kasar Sin ta jami'ar fasahohi ta Sydney, ya ce, yanayin bangaren sayar da kayayyakin kasar na da kyau sosai. Hakan, a cewarsa, abu ne mai muhimmanci sosai, ganin yadda kasar ta sauya manufarta zuwa kasa mai dogaro kan bangaren saye da sayarwa a kokarin raya tattalin arzikinta.
Tattalin arzikin kasar Sin na cikin yanayi mai kyau a farkon shekarar 2019, inda alkaluma ke nuna yanayi mai inganci a rubu'in farkon shekarar bana.
Laurenceson ya ce, kasar za ta iya samun karin ci gaba ta fuskar tattalin arziki bisa matakanta na kara bude kofa ga kasashen waje, gami da gyare-gyaren da take ci gaba da aiwatarwa a kasuwannin cikin gida. (Bello Wang)