Da yake karin haske, jami'in dake kula da dakin ajiye kayayyakin tarihin Huang Keli, ya bayyana cewa, za kuma a bude manyan dakunan nune-nune guda 4 dake dakin a wannan lokacin, wadanda suka mayar da hankali kan taken, "tekun zamanin da" da teku a yau" "gwagwarmayar gano tekun" da "zamanin dragon" da sauransu.
Masu ziyara za su fahimci alakar dake tsakanin teku da rayuwa, abubuwan da aka binciko a karkashin teku, rayuwar halittun ruwa da muhalli da ci gaba mai dorewa.
A lokacin gwajin, za a bar masu ziyara 3,000 a kowa ce rana. Ana kuma bukatar masu sha'awar kawo ziyara, su sayi tikiti ta shafin intanet din da aka tanada ko manhajar Wechat, wadanda za a bude a a ranar 28 ga wata.
Dakin mai hawa uku, ya kai girman murabba'in sq mita 150,000, yana kuma da manyan yankunan wurare baje kolin kayayyakin guda 6 da manyan dakunan nune-nune guda 15. (Ibrahim)