Da yake bayyana muhimmancin dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika, Li Keqiang ya ce a shirye kasar Sin take ta yi aiki da Habasha wajen zurfafa hadin gwiwarsu karkashin Ziri Daya da Hanya Daya da kuma aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika da aka yi a bara.
Ya ce kasar Sin ta shirya zurfafa hadin gwiwa da Habasha a fannonin samar da ababen more rayuwa da mara baya ga raya yankunan da layin dogon da ya tashi daga Addis Ababa zuwa Djibouti ya ratsa, yana mai cewa za a karfafawa kamfanonin kasar Sin gwiwar zuba jari a Habasha.
A nasa bangaren, Firaminista Abiy Ahmed, ya ce Habasha na daukar Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar hulda, kuma a shirye take ta inganta hadin gwiwarta da Sin a fannoni daban daban, domin zama abun misali ga kungiyar kasashe masu tasowa da kuma hadin gwiwar Sin da Afrika. (Fa'iza Mustapha)