in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rancen kasar Sin a bangaren ayyukan da ba sa gurbata muhalli ya samu tagomashi a rubu'in farko na bana
2019-04-28 16:01:26 cri
Babban bankin kasar Sin ya ce, hada-hadar kudade a bangaren ayyukan da ba sa gurbata muhalli a kasar, ya samu tagomashi a rubu'in farko na bana.

Basussukan a bangaren, cikin kudin Sin wato Yuan da kudaden kasashen waje, ya kai yuan triliyan 9.23, kwatankwacin dala triliyan 1.37 ya zuwa watan Maris, adadin da ya karu da kaso 4.3 daga farkon shekara, wanda kuma ya dauki kaso 9.9 na jimilar adadin.

Daga farkon bana, rance da aka bayar a bangaren ayyukan sufuri da ba sa gurbata muhalli ya kai triliyan 4.1, wanda ya karu da kaso 4.8, yayin da na bangaren makamashi mai tsafta da ake iya sabuntawa, ya kai yuan triliyan 2.28, adadin da ya karu da kaso 1.7.

Hada-hadar kudade a bangaren raya muhalli na samun ci gaba la'akari da cewa an karfafawa bankuna gwiwar bada rance a bangaren raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba.

A shekarar 2018, bashin da ake bi a bangaren ya kai yuan triliyan 8.23, wanda ya karu da kaso 16 a kan na bara, sannan kuma ya dara na dukkan basussukan bangaren da ba na hada-hadar kudi ba da sauran bangarori da kaso 6.1. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China