Rahoton ya kara da cewa, kotun kolin ta kara daukar wasu matakai kan yadda za a rika hukunta manyan laifuffuka da suka shafi gurbata muhalli.
A wani labarin kuma, kotun kolin al'ummar ta bayyana cewa, kotuna dake sassan kasar, sun yanke hukunci mai tsauri kan wadanda ake zargi da aikata laifuffuka da suka shafi gurbata muhalli, inda a shekarar 2018, kotunan suka yanke hukunci kan irin wadannan laifuka har guda 2,204.
Haka kuma kotuna a sassa daban-daban na kasar Sin, sun yanke hukunci kimanin 251 kan laifukan da suka shafi muhalli da albarkatu. (Ibrahim Yaya)