Babbar darektar hukumar Maimunah Mohd Sharif, ita ce ya yi wannan yabo,yayin kaddamar da wata makala mai taken "Raya birane ta hanyar farfado da kogunan birane da suka gurbace, a koyi darasi daga kasar Sin da sauran kasashe". Ta ce, kwararan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka, sun taimaka wajen dawo da kogunan dake biranen kasar, saboda barazanar da suke fuskanta, sakamakon bunkasar masana'antu.
A don haka, jami'ar ta yaba da matakan da mahukuntan kasar ta Sin suka dauka wajen bullo da managartan matakai, da kudade don kara ingancin kogunan dake biranen kasar.
Shirin kare muhalli na MDD da jami'ar Tongji dake birnin Shanghai na kasar Sin ne suka gabatar da makalar tare, aka kuma kaddamar da ita a gefen zaman taro na hudu kan muhalli na MDD dake gudana yanzu haka a birnin Nairobin kasar Kenya.
Makalar ta nuna cewa, amfani da fasahohin da aka zayyana gami da manufofin kirkire-kirkire, sun taimaka wajen sake dawo da koguna dake biranen kasar Sin.(Ibrahim)