in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bada rahoton samun ingancin iska a 2018
2019-04-22 09:33:34 cri
Ma'aikatar kula da muhalli ta kasar Sin, ta ce ingancin iska na ci gaba da kyautata a kasar, la'akari da raguwar abubuwa masu gurbata iskar.

A rahoton da ya mikawa majalisar wakilan al'ummar kasar domin yin nazari yayin zamanta dake gudana, Ministan kula da muhalli da halittu na kasar Li Ganjie, ya ce daga cikin birane 338 na kasar Sin, 121 sun kai mizanin ingancin iska a 2018.

A cewar Li Ganjie, an samu kyautatuwar ingancin iska sosai a muhimman yankunan, duk da cewa an samu gurbatar iskar a lokacin hunturu da kaka.

Matsakaicin yawan ma'aunin gurbartar iska na PM2.5, ya sauka da kaso 11.8 a shekarar 2018 a yankunan Beijing da Tianjin da Hebei da kewayensu.

Jami'in ya kara da cewa, a matsakaicin mataki, biranen 338 sun samu ingantacciyar iska fiye da gurbatacciya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China