Hukumar dake lura da shuka itatuwa ta birnin Beijing, ta ce an gudanar da manyan ayyuka, na fadada yawan itatuwa da tsirrai da ake shukawa a sassan birnin, inda a shekarar da ta gabata, fadin dajin dake birnin ya kai hekta 17,933, aka kuma kara sassan shuke shuke, da fadin su ya kai hekta 710.
Hukumar ta ce ya zuwa karshen shekarar 2018 da ta gabata, fadadar gandun dajin birnin ta kai kaso 43.5 bisa dari, haka kuma fadadar yankunan shuke shuke a kewayen birnin ta kai kaso 48.4 bisa dari, yayin da yawan shuke shuke, idan an danganta da yawan al'ummun birnin za su kai sakwaya-mita 16.3.(Saminu)