in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samar da ilmin fasahar kere kere sama da 800 wanda ya samu karbuwa a duniya
2018-06-13 10:58:39 cri
Ma'aikatar ilmin kasar Sin ta sanar da cewa jami'o'in kasar sun bada shaidar digiri sama da 800 a fannin fasahar kere kere wanda ya samu karbuwa kuma ya shiga cikin jerin mafiya inganci a duniya.

Ma'aikatar ta ce cibiyar kula da manyan makarantun ilmi da sashen nazarin ilmin fasahar kere kere na kasar Sin ne suka tantance digirorin kimanin 846 wadanda jami'o'in kasar Sin kimanin 198 da wasu kwalejojin kasar suka bayar shaidar karatun ya zuwa karshen shekarar 2017.

Kasancewar kasar Sin tana da ruwa da tsaki game da yarjejeniyar nan ta Washington, kana kasashen duniya da wasu shiyyoyi na duniya 18 ma suna da ruwa da tsaki a bangaren tantance ingancin ilmin, kamar yadda ma'aikatar ilmin ta Sin ta tabbatar da hakan. Yarjejeniyar gamayyar kasa da kasar tana taimakawa wajen daga martabar ilmin fasahar kere kere da kuma samar da kwararru a wannan fanni na fasaha a kasa da kasa.

Sama da mutane miliyan 1.2 ne suke kammala karatun digirinsu na farko a fannin ilmin fasahar kere kere daga jami'o'in kasar Sin a duk shekara.

Kasar Sin ta kai wani mataki na bunkasa ilmin fasahar kere kere tun a wasu 'yan shekaru da suka gabata. Shiri na baya bayan nan da aka bullo da shi a fannin ilmin fasahar kere kere shi ne wanda aka kaddamar da shi a shekarar 2017. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China