in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#BRF2019# Xi Jinping: Sin za ta dauki muhimman matakan kara bude kofarta ga kasashen waje
2019-04-26 10:46:25 cri
A wajen taron kolin hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu ko kuma BRF a takaice wanda aka kaddamar da shi yau Jumma'a a Beijing, shugaba Xi Jinping ya ce, kasarsa za ta dauki wasu manyan matakan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da kyautata tsare-tsare, a wani kokari na kyautata ayyukan bude kofa ga kasashen waje. Matakan sun hada da, fadada bangarorin da za'a iya shigowar jarin waje, da karfafa hadin-gwiwar kasa da kasa a fannin kare 'yancin mallakar fasaha, da fadada ayyukan shigo da kayayyaki da hidimomi daga kasashen waje, da daidaita manufofin tattalin arzikin kasa da kasa daga manyan fannoni, tare kuma da kara maida hankali kan aiwatar da manufofin bude kofa ga kasashen waje. (Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China