in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru: Shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da damammaki ga kasashen da suka rungumi shawarar
2018-01-18 10:46:26 cri

Babban jami'in kula da harkokin zuba jari na kamfanin KraneShares mai kula da harkokin kadarori na Amurka, Brendan Ahern, ya bayyana cewa, shawarar ziri daya da hanya daya za ta karfafa harkokin kasuwanci da cinikayya tsakanin kasashen da suka rungumi shawarar.

Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin taron kolin da kamfanin CICC, kamfanin da ya kware a fannin kudaden musayar cinikayyar kasar Sin da hukumar kula da harkokin kudi da zuba jari ta kasa da kasa ta kasar Sin suka shirya game da shawarar ziri daya da hanya daya a birnin New York, ya ce, shawarar wadda za ta kushi kasashe sama da 70 za kuma ta karfafa alakar diflomasiya da kuma al'adu tsakaninsu.

Wani rahoto da kamfanin ya fitar ya nuna cewa, kasashe dake cikin wannan shawara, suna bukatar zuba jari, domin su bunkasa kasashensu da ma inganta kayayyakin more rayuwa. Yayin da a hannu guda shawarar za ta samar da damammakin na cinikayya da zuba jari a bangaren samar da kayayyaki ga gine-gine, matakin zai kuma baiwa kasar Sin wata sabuwar hanyar fadada kayayyakin da take fitarwa.

Shi ma shugaban kamfanin na KraneShares Jonathan Krane ya ce, da alamun shawarar za ta haifar da karuwar harkokin zuba jari triliyan 6 a sassan kasashen dake cikin ta, kimanin kaso 34 cikin 100 na GDPn duniya.

Daga karshe rahoton kamfanin ya nuna cewa, shawarar ziri daya da hanya daya za ta canja makomar tattalin arzikin karni na 21.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China