in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin sa hannu kan takardar fahimtar juna game da shawarar 'Ziri daya da hanya daya'
2017-09-23 13:52:30 cri
Jiya Juma'a a hedkwatar MDD, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da babban sakataren MDD Antonio Guterres, sun halarci bikin sanya hannu kan takardar fahimtar juna game shawarar 'Ziri daya da hanya daya' a tsakanin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da sashen kula da harkokin tattalin arziki da al'umma na MDD.

Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Liu Jieyi, da mataimakin babban sakataren MDD Liu Zhenmin sun rattaba hannu kan takardar da ke shafar hakikanin hadin kai, karfafa kwarewa, more fasahohin da aka samu, nazarin manufofi da dai sauransu, wadda kuma ake fatan zata karfafa hadin kai a tsakanin bangarorin biyu, da taimakawa kasashe masu tasowa dake kan hanyar 'Ziri daya da hanya daya' wajen kara karfinsu na samu bunkasuwa, tare kuma da inganta raya 'Ziri daya da hanya daya' da tabbatar da ajendar neman dauwamamman ci gaba nan da shekarar 2030.

A shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar hadin kai ta 'Ziri daya da hanya daya', wadda ta samu goyon bayan kasa da kasa. A watan Yunin bana a nan birnin Beijing, an cimma nasarar shirya taron kolin dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa game da shawarar, inda aka samu jerin nasarori. Ya zuwa yanzu dai, kasar Sin ta riga ta sanya hannu kan takardun hadin kai game da 'Ziri daya da hanya daya' tare da kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa kimanin 74. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China