in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar Ziri daya da hanya za ta taimakawa kasashen aiwatar da manufofin MDD
2017-12-04 10:32:21 cri
Shugaban sashen kula da harkokin gwamnatoci a shirin kare muhalli na MDD(UNEP) Jamil Ahmad, ya ce shawarar nan ta Ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta bullo da ita, za ta taimakawa kasashen da abin ya shafa cimma manufofi samun ci gaba mai dorewa.

Jami'in na MDD wanda ya shaidawa manema labarai hakan a birnin Nairobin kasar Kenya, ya ce hanyar tattalin arziki ta Siliki da hanyar Siliki ta teku na karni na 21 da shirin muradin karni su ma za su taimaka.

Ahmad ya ce shawarar ziri daya da hanya daya ta nuna kyakkyawan misali kan yadda za a fara aiwatar da ayyukan da suka shafi manufofin muradun karni wanda ke da nufin inganta rayuwar al'ummar duniya. Ita dai wannan shawara ta kunshi, hanyar tattalin arziki ta Siliki da hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21. Kuma an kirkiro ta ne da nufin bunkasa harkokin cinikayya, zuba jari da gina kayayyakin more rayuwa a yankunan Asiya da Turai da kuma Afirka wadanda suka ratsa tsohuwar hanyar ciniki ta Siliki har ma fiye.

Ahmad ya ce, shawarar ziri daya da hanya daya da kuma manufofin muradun karni, duk sun mayar da hankali ne kan ginshikai guda biyar, wadanda ke da nufin inganta rayuwar al'ummar duniya baki daya.

Jami'in ya ce, shirin kare muhalli na MDD zai tabbatar cewa, an sanya batun kare muhalli a cikin dukkan wasu bangarori na ayyuka da shirye-shiryensa.

Shirin kare muhalli na MDD ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da kasar Sin game da yadda za a samar da matakan aiwatar da ayyuka marasa gurbata muhalli da ci gaba mai dorewa a yankunan da ke cikin shawarar ziri daya da hanya daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China