in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar ziri daya da hanya daya ta bude sabon shafin hadin gwiwar kasa da kasa
2019-04-12 13:28:16 cri

A ranar Alhamis jakadan kasar Sin ya sanar da cewa, shawarar ziri daya da hanya daya ta bude wani sabon shafin hadin gwiwar kasa da kasa.

"Shawarar ziri daya da hanya daya ta bude sabon shafin hadin gwiwar kasa da kasa, ta zamanto wata sabuwar jagora wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, ta kasance wani muhimmin dandalin kulla dangantaka a tsakanin kasashen duniya, kana ta kasance a matsayin wata muhimmiyar dama wajen samar da guraben ayyukan yi ga kasashen duniya," Ma Zhaoxu, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, shi ne ya bayyana hakan a lokacin babban taron MDDr wanda aka shirya domin murnar tunawa da cika shekaru 100 da kafuwar kungiyar kwadago ta kasa da kasa wato (ILO).

"Yankunan hadin gwiwa kimanin 82 da kasar Sin ta gina tare da kasashen duniya bisa shawarar ta ziri daya da hanya daya sun samar da guraben ayyukan yi kusan dubu 300." in ji shi.

Da yake jawabi game da taron dandalin hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu, wanda za'a gudanar a karshen watan Afrilu a birnin Beijing, wakilin na Sin ya ce, "Muna da kwarin gwiwa cewa wannan dandali zai kara kaimi ga hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya hanya daya kuma zai bayar da babbar gudunmowa wajen samar da ingantaccen tsarin aiki ga kowa da kowa."(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China