in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da yara miliyan 175 ne ba su shiga makarantar kafin firamare ba
2019-04-10 13:52:29 cri
Asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF), ya ce sama da yara miliyan 175, kusan rabin adadin yaran da suka isa shiga makaranta a duniya ne ba su shiga makarantar kafin firamare ba.

A cewar rahoto na farko kan ilimin kafin firamare da UNICEF ya taba hadawa, matsalar ta fi yawa a kasashen dake da karancin kudin shiga, inda yaro 1 cikin yara 5 ne kadai ke shiga makarantar kafin firamare.

Rahoton ya bayyana cewa, akwai yiwuwar yaran da aka sanya a makarantar kafin firamare a bara, su samu basira mai muhimmanci da suke bukata wajen samun nasara a makaranta.

Rahoton ya ce arzikin gida da ilimin mahaifiya da wurin da ake zaune, na daga cikin muhimman abubuwan dake tantance shigar yara makaranta. Sai dai, talauci shi ne abu daya tilo mafi girma dake tantance batun shiga makarantar.

UNICEF na kira ga gwamnatoci su samar da shirin bayar da ingantaccen ilimin kafin firamare na bai daya, na a kalla shekara guda, wanda zai shiga cikin matakan ilimin ko wane yaro, musammam ga yara masu rauni da wadanda ake nuna musu wariya.

Domin cimma wannan, UNICEF na bukatar gwamnatoci su ware a kalla kaso 10 na kasafin kudinsu na ilimi domin inganta ilimin farko ga yara da kara kwarewa da yawan malamai da kuma samar da ingantaccen ilimi ga kowa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China