in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yutu-2 na kasar Sin zai yi aiki fiye da yadda aka tsara shi
2019-03-14 10:25:40 cri

Cibiyar kula da taurarin dan Adam da shirin binciken sararin samaniya na hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta kasar Sin, ta bayyana cewa, kumbon binciken sararin samaniya na kasar Sin Yutu-2 ko Jade Rabbit-2, ya yi tafiyar mitoci 163 a bangaren duniyar wata mai nisa, ana kuma sa ran zai yi aikin fiye da watanni ukun da aka tsara tun farko.

A jiya ne dai, Yutu-2 da Chang'e- 4 suka daidaita karfin lantarkin da suke amfani da shi, saboda tsananin sanyin da ake yi da dare. A ranar 3 ga watan Janairu ne, Chang'e-4 ya sauka a yankin Von Karman na kudancin Antatika mai tsananin sanyi dake nesa da duniyar wata.

Na'urar binciken ta gudanar da binciken kimiyya kan wasu duwatsu a bangaren duniyar wata mai nisa, matakin da ake fatan zai taimakawa masana kimiyya gano ko sun fito ne daga duniyarmu ko kuma duniyar wata

Kumbon na Jade Rabbit-2 mai nauyin kilogram 135, shi ne na farko da ya fara sauka a bangaren duniyar wata mai nisa, kana kumbo maras nauyi da aka taba harbawa duniyar wata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China