in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kaddamar da gangamin samar da kariya ga yara dake rayuwa a yankuna masu fama da rigingimu
2019-04-03 10:34:49 cri
A jiya Talata ne MDD ta bayyana kaddamar da wata sabuwar manufa, ta yayata bukatar samar da kariya ga yara dake rayuwa a yankuna masu fama da tashe tashen hankula.

Sakataren MDD mai lura da bukatun yara, da tashe tashen hankula Virginia Gamba ne ya kaddamar da manufar, yana mai cewa hakan zai karfafa hadin gwiwa tsakanin MDD, da kungiyoyin fararen hula, da ma sauran sassan kasa da kasa nan da shekaru uku masu zuwa.

Da yake karin haske game da hakan, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce matakin zai samar da zarafi na aiwatar da manufofi daban daban, wadanda za su dakile cin zarafin yara dake rayuwa a irin wadannan yankuna masu shan fama da rigingimu.

Manufar da aka yiwa lakabi da "Aiki domin ba da kariya ga yara dake rayuwa a yankuna masu fama da rigingimu." ta samu yabo daga babban magatakardar MDD Antonio Guterres, wanda ya ce yayata ta, zai haifar da wayewar kai ga al'ummar duniya, game da bukatar baiwa yara kariya a matakin farko, tun ma kafin su tsinci kan su cikin mawuyacin hali. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China