in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fitar da kananan kabilu 3 daga kangin talauci
2019-04-22 09:20:10 cri

Kasar Sin ta fitar da rukunonin kananan kabilu 3 daga kangin talauci a lardin Yun'nan dake kudu maso yammacin kasar, yayin da take kara kaimi ga cimma burin fatattakar talauci baki daya, ya zuwa shekarar 2020.

Bisa alkaluman kidayar da aka yi a 2010, rukunonin kananan kabilun da suka hada da Dulong da De'ang da Jino na da jimiliar al'ummomi 50,000.

Yawan mutanen dake fama da talauci ya ragu daga kaso 24.25 a 'yan shekarun baya, zuwa kaso 2.42, adadin da ya yi kasa da kaso 3 da ake bukata na cire su daga jerin masu fama da talauci a yammacin kasar Sin.

Kabilun na zaune ne a yankuna masu tsaunuka na sassan lardin Yun'nan, inda kabilar Dulong ke yankin arewa maso yammaci, kabilar De'ang a yankin yammaci yayin da kabilar Jino ke yankin kudancin lardin.

Huang Yunbo, shugaban ofishin yaki da talauci da samar da ci gaba na lardin, ya ce a bana, za a cire jimilar kananan kabilu 7 daga jerin masu fama da talauci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China