Gwamnatin kasar Sin ta dauki kwararan matakai a shekarar 2018 wajen tabbatar da kyautata yanayin zaman rayuwar al'ummar kasar masara galihu wadanda ke rayuwa cikin yanayin talauci, kamar yadda ma'aikatar kula da walwalar jama'a ta kasar ta bayyana. Ma'aikatar ta kashe kudade kimanin yuan biliyan 2.25 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 335 wajen gudanar da muhimman ayyukan kyautata jin dadin rayuwar jama'a a wasu larduna 22 mafiya fama da talauci a kasar, wanda jimillar ya tasama kashi 80 bisa 100 na adadin kudin da kasar Sin ta kashe wajen gudanar da ayyukan yaki da fatara a shekarar 2018, in ji ma'aikatar.
Ma'aikatar dai ta kyautata rayuwar mutanen dake cikin matsanancin yanayi na bukata, da kuma masu bukata ta musamman ta hanyar ba su kudaden alawus domin kula da rayuwar iyalansu.
Ya zuwa yanzu, mafi karanci kudaden alawus da ake bayarwa a kasar ya wuce matakin da hukumar yaki da fatara ta kasar ta tsara tun da farko. (Ahmad Fagam)