in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa asusun tallafawa matalauta ta hanyar kiyaye halittu na farko a Sin
2019-03-19 14:09:15 cri
An samu labari cewa, kwanan baya hukumar kula da sana'ar gandun daji da filin ciyayi ta kasar Sin, ta kafa asusun musamman na kawar da talauci ta hanyar kiyaye halittu na sana'ar gandun daji da filin ciyayi a kasar Sin, asusun da ya kasance asusun tallafawa na farko a fannin kawar da talauci ta hanyar kiyaye halittu a nan kasar Sin.

Asusun din zai mai da hankali kan yankuna mafiya fama da talauci, da gundumomi masu fama da talauci a karkashin shugabancin hukumar, da kuma wasu yankuna masu fuskantar zaizayewar kasa mai nasaba da yaduwar hamada, za kuma yi amfani da asusun ne domin ba da tallafi a fannin halittu, da dasa itatuwa da ciyayi, da kuma kawar da talauci ta hanyar raya sana'ar halittu da dai sauransu, domin cimma burin kyautata muhallin halittu da kawar da talauci.

Ya zuwa yanzu, an riga an samar da kudin RMB biliyan 108.5 kan sana'ar gandun daji a yankuna masu fama da talauci, kana da zabar masu fama da talauci sama da dubu 500 don gudanar da aikin kiyaye gandun daji, tare kuma da taimakawa masu fama da talauci miliyan 1.8 don kara samun kudin shiga. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China