Babbar hukumar samar da lantarki ta kasar Sin ne ta tabbatar da hakan a ranar Asabar cewa, an kaddamar da fara amfani da lantarkin ne a farkon watan Afrilu, da nufin amfanawa mutanen dake fama da talauci sama da 2,400 a yankin.
A gundumar Hongyuan dake yankin Tibet da Qiang na Aba mai cin gashin kai, za'a kafa cibiyar samar da lantarki mai aiki da hasken rana ta megawatt 20, wadda ake sa ran za ta samar da karfin hasken lantarki sama da megawata miliyan 26.24 a duk shekara.
Mazauna gundumar za su yi amfani da lantarkin, kana za'a sayar da ragowar ga sashen kula da hasken lantarki, wanda ake sa ran za ta taimaka wajen kara samar da kudaden shiga a kalla yuan dubu 1 a duk shekara ga duk wanda ke fama da talauci.
An kaddamar da aikin yaki da talauci a yankin Sichuan ne ta hanyar samar da lantarki daga hasken rana a karshen shekarar 2017. An yi kiyasin za'a gudanar da wasu ayyukan kimanin 19 a yankunan. Aikin na gundumar Hongyuan shi ne na farko da aka kaddamar kawo yanzu. (Ahmad Fagam)