in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi alkawarin bada gagarumar gudunmawa ga shirin yaki da fatara a duniya
2017-10-10 10:34:56 cri
Mataimakin firaiministan kasar Sin Wang Yang, ya sanar a jiya Litinin cewa, kasarsa za ta bayar da gagarumar gudunmowa ga shirin yaki da talauci a duniya.

Da yake jawabi yayin wani dandali, Wang ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance wata kasa mai matukar goyon baya da kuma nuna jajurcewa game da yaki da fatara a duniya baki daya.

Ya ce kasar Sin za ta yi musayar kwarewa da kuma irin ci gaban da ta cimma tare da yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen tabbatar da ganin an cimma nasarar ajandar nan ta samar da dawwamamman ci gaban duniya nan da shekarar 2030.

Bayan jan aikin da ta gudanar a shekaru masu yawa, sannu a hankali kasar tana gab da cimma burinta na samar da al'umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni nan da shekarar 2020, inda kasar ke fatar tsame dukkan jama'arta dake fama da kangin talauci.

Sama da Sinawa miliyan 10 ake tsamewa daga kangin fatara a duk shekara tun daga shekara ta 2012 kawo yanzu.

Ya zuwa karshen shekarar 2016, akwai ragowar 'yan kasar kimanin miliyan 43.35 wadanda kudin shigarsu na shekara ke kasa da yuan 2,300 kwatankwacin dalar Amurka 344, kusan kashi 3 bisa 100 na yawan al'ummar kasar.

Taron dandalin da aka gudanar ya samu halartar sama da mutane 200, ciki har da jami'an gwamnati daga kasashe13 da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa kimanin 16. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China