in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hafsoshin soji daga nahiyar Afrika sun fara ziyarar mako guda a kasar Sin
2019-04-22 09:13:37 cri
Tawagar matasan hafsoshin jami'an soji 100, daga kasashen Afrika da Tarayyar Afrika AU, sun fara ziyarar mako guda a kasar Sin daga jiya Lahadi, bisa gayyatar ma'aikatar tsaro ta kasar Sin.

Ana sa ran ziyarar za ta inganta musayar dabaru tsakanin hafsoshin na Afrika da takwarorinsu na kasar Sin, da zurfafa abota tsakanin rundunonin sojin Sin da Afrika da kuma karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu a fannin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Hafsoshin sojin na Afrika, za su kai ziyara kwalejoji da sansanoni da masana'antun rundunar sojin kasar Sin.

Za kuma su saurari lakca kan maudu'ai daban daban, ciki har da kawancen soji karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China