in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron Nijeriya ya lashi takobin fadada hadin gwiwa da kasar Sin
2018-10-24 09:39:32 cri
Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma Ministan tsaron kasar janar Wei Fenghe, ya gana a jiya Talata da Ministan tsaron Nijeriya Mansur Dan Ali a nan birnin Beijing, inda suka halarci taron tattaunawa na Xiangshan karo na 8, wanda ke tattauna batutuwan tsaro tsakanin kasa da kasa.

Wei Fenghe, ya ce kasar Sin na maraba da Nijeriya ta shiga a dama da ita cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

Ya ce kokarin da shugabannin kasashen biyu suka yi, ya kai ga samun manyan nasarori a dangantakar dake tsakanin rundunonin sojin kasashen.

Har ila yau, ya yi kira ga bangarorin biyu su kara aminta da juna da bunkasa musayar bayanai da hadin gwiwa tare da daukaka matsayin dangantakar rundunonin sojinsu.

A nasa bangaren, Mansur Dan-Ali ya godewa kasar Sin bisa taimakon da take ba Nijeriya a fannin bunkasa ababen more rayuwa da tsaron kasa, yana mai cewa, a shirye Nijeriya take ta inganta hadin gwiwarta da kasar Sin a fannonin wanzar da zaman lafiya a duniya da horar da jami'ai da bunkasa kimiyya da fasahar ayyukan soji. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China