Ma'aikatar tsaron kasar Sin ce mai karbar bakuncin taron, kana mahalarta taron sun hada da wakilan sojojin kasar Sin, da na hukumomin tsaro, da sojoji na kasashe 50 dake nahiyar Afirka, da na kungiyar tarayyar Afirka AU.
An saka wa taron taken "Hadin gwiwa, da taimakon juna", inda a wajen taron na yini 15, za a tattauna batutuwan da suka hada da tsaron wasu shiyyoyi, da aikin raya harkar tsaron kasa a nahiyar Afirka, da hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka ta fuskar tsaro.
A wajen bikin kaddamar da taron, darektan ofishin hadin gwiwar kasa da kasa a fannin aikin soja karkashin kwamitin aikin soja na tsakiya na kasar Sin Hu Changming, ya yi wani jawabi a madadin bangaren kasar Sin, inda ya ce, kasar Sin za ta tsaya kan ra'ayin da ta dauka a fannin harkar tsaro na hadin gwiwa, na zama mai dorewa, sa'an nan za ta kara yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a wannan fanni, da kokarin daga wannan hadin gwiwar zuwa wani sabon matsayi. (Bello Wang)