in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron Sin ya gana da wakilan dindindin na mambobin kwamitin tsaron MDD
2018-11-26 21:09:15 cri
Mamban majalissar zartaswar kasar Sin kana ministan tsaron kasar, Wei Fenghe, ya gana da wakilan dindindin na mambobin kwamitin tsaron MDD a Litinin din nan, yayin ziyarar da suke yi a kasar Sin.

Da take tsokaci yayin ganawar, Wei ya ce Sin na martaba tsarin cudanyar kasashen duniya karkashin MDD, kuma a ko da yaushe, rundunar sojin Sin na bin tafarkin samar da ci gaba cikin yanayin zaman lafiya.

Kaza lika Wei Fenghe ya ce Sin a shirye take, ta yi aiki da sauran kasashen duniya wajen bunkasa hadin kai a fannin wanzar da zaman lafiya, da samar da yanayi na tsaro bisa daidaito, da zaman lafiya, da cin gajiya tare da raba nasara, baya ga hada hannu wajen gina al'umma mai makomar bai daya ga dukkan bil Adam, da kuma samar da duniya mai wanzajjen tsaro, da zaman lafiya, da lumana, a mataki na kasa da kasa da na shiyya shiyya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China