in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron dandali na Xiangshan
2018-10-27 16:46:27 cri
An rufe taron dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na takwas a nan birnin Beijing a jiya Juma'a, inda mahalarta taron suka cimma daidaito game da jigon taron, wato "kulla huldar abota ta zaman daidaito da aminci da juna da kuma hadin gwiwa da kuma samun moriyar juna".

Mr. Chen Guangjun, shugaban kwalejin nazarin manufofin kasa da kasa na kasar Sin ya ce, "Ba za a kai ga cimma moriyar juna ba, muddin ba a tabbatar da zaman daidaito da aminci da shawarwari da kuma hadin gwiwa da juna ba, sa'an nan dauwamammen tsaro zai samu ne yayin da ake kiyaye ci gaban juna". Ya kara da cewa, hada kan kasa da kasa a kokarin kiyaye zaman lafiyar duniya, niyyar kasar Sin ce da ba ta taba sauyawa ba.

Yayin taron dandalin na wannan karo, mahalarta sun kuma yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan da suka hada da "sabbin hanyoyin kula da harkokin tsaro a duniya" da "barazanar ta'addanci da matakan tinkararta", da "hadin kai a fannin tsaron teku" da "Kalubalen da aikin kiyaye zaman lafiya na MDD ke fuskanta da hadin gwiwar da za a aiwatar" da dai sauransu. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China