in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Angola ya yaba wa goyon bayan Sin ga kasarsa
2019-04-18 11:21:25 cri

Jiya Laraba 17 ga wata, shugaba João Manuel Gonçalves Lourenço na kasar Angola, ya nuna yabo da kuma godiya ga goyon bayan da kasar Sin ta dade tana bayarwa kasarsa ta fuskar raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa.

Shugaba Lourenço ya fadi haka ne, a yayin da ya karbi takardar aiki ta sabon jadakan Sin a kasar sa Gong Tao a fadar shugaban kasar. Shugaban Angola ya ce, hukumomin gwamnatin kasar za su tuntubi, da taimaka wa ofishin jadakancin kasar Sin da ke kasar, wajen kara azama kan hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2 a sassa daban daban, a kokarin kara raya huldar da ke tsakaninsu.

A nasa bangaren kuma, Gong Tao ya ce, kasar Sin ta sa muhimmanci kan huldar da ke tsakaninta da Angola, tana kuma son hada kai da Angola wajen aiwatar da muhimmin ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma, da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka, da gaggauta kyautata hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakanin kasashen 2, a kokarin bunkasa huldar abota da ke tsakanin kasashen 2 daga manyan tsare-tsare zuwa sabon mataki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China