in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da shugaban kasar Angola
2018-01-14 13:06:57 cri

A daren ranar 13 ga wata, shugaban kasar Angola Joao Lourenco, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a fadarsa.

A yayin ganawar, Wang Yi ya bayyana cewa, ranar 12 ga wata rana ce ta cika shekaru 35 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Angola. A cikin shekaru 35 da suka gabata, Sin da Angola sun yi imani da juna a fannin siyasa, da nuna goyon baya ga juna kan batutuwan dake shafar moriyarsu, da bunkasa hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. A halin yanzu, kamata ya yi bangarorin biyu su takaita fasahohin da suka samu, da kirkiro sabbin hanyoyin samun moriyar juna, da fadada hadin gwiwarsu a sabbin fannoni don sa kaimi ga raya hadin gwiwarsu zuwa wani sabon matsayi. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga kamfanonin kasarta da su zuba jari a kasar Angola da yin hadin gwiwa, kana tana fatan kasar Angola za ta tabbatar da moriyar kamfanonin Sin bisa tsarin bin dokoki.

A nasa bangare, shugaba Lourenco yana fatan kasar Sin za ya ci gaba da nuna goyon baya wajen aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa ciki har da zirga-zirgar hanyoyin jiragen kasa na kasar Angola, kana yana maraba da kamfanonin Sin da su je kasar Angola don yin hadin gwiwa a tsakaninsu da kasar a fannonin hakar ma'adinai, aikin gona, kiwon dabbobi, yawon shakatawa da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China