An ce, jam'iyyar 'yantar da jama'ar kasar Angola ta sanar da wannan kuduri a wajen taron musamman da aka gudanar a birnin Luanda dake kasar.
Lourenco ya gudanar da ayyukan harkokin jam'iyyar da majalisar dokokin kasar a dogon lokaci, ya zama ministan tsaron kasar tun daga shekarar 2014, kuma ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar 'yantar da jama'ar kasar Angola tun daga watan Agusta na shekarar 2016. A ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 2017, Lourenco ya yi rantsuwar kama aiki na shugabancin kasar ta Angola. (Zainab)