in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatan jinya a kasar Angola sun shiga yajin aikin gama gari
2018-06-12 09:41:17 cri
Ma'aikatan jinya a Luanda babban birnin Angola, sun shiga yajin aikin gama gari na sai baba-ta-gani, inda suke bukatar a biya su basussukan da suke bi, tare da gyara musu albashi da sauran alawus-alawus.

Kungiyar Sintenfl, ta ma'aikatan jinya ta kasar ce ta kira yajin aikin, kamar yadda sanarwar da sakatare janar na kungiyar, Afonso Kileba ya fitar, ta bayyana.

Sanarwar ta jadadda cewa, wa'adin yajin aikin zai dogara ne kan lokacin da gwamnati ta biyawa ma'aikatan bukatun da suka gabatar.

Kungiyar Sintenfl, na da jimlar ma'aikatan jinya dake karkashinta guda 6,000 a lardin dake da mazauna kimanin miliyan 7. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China