in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'i: Angola tana ci gaba da zama matattarar safarar hauren giwa ta haramtattun hanyoyi
2018-07-26 10:05:08 cri
Babban sakataren kula da albarkatun gandun daji na kasar Angola Andre de Jesus Moda ya ce, har yanzu kasar ta Angola tana ci gaba da zama a matsayin wata babbar matattarar da ake yin fataucin hauren giwa, da kahon bauna, da dabbobin pangolin, da gwaggwon biri da tsuntsayen daji ta haramtattun hanyoyi.

Jami'in ya sanar da hakan ne cikin jawabin da ya gabatar a Luanda babban birnin kasar a lokacin taron tawagar kwararru karo na biyu game da aiwatar da manufofin kungiyar tarayyar Afrika na yaki da cinikin sassan jikin dabbobin daji ta haramtattun hanyoyi.

A cewar sakataren hukumar, a shekarar 2017 kadai an samu cinikin hauren giwa da sauran sassan jikin dabbobin daji wadanda aka yi farautarsu da ya kai ton 1.2.

Jami'in ya ce masu farautar dabbobin da suka shiga dazukan Angola sun fito ne daga kasashen duniya daban daban.

Ya bayyana cewa doguwar hanyar tekun kasar, da hanyoyin kan tudu da hanyoyin iyakokin sararin samaniyar kasar suna bukatar a samar da kudade domin tabbatar da tsaronsu da kula da su da kuma kiyaye su.

Kasar Angola tana karbar bakuncin taron kwararru na Afrika game da aiwatar da dabarun yaki da masu hallaka dabbobin dawa da yin cinikin sassan jikin dabbobin ta haramtattun hanyoyi na Afrika wanda ake gudanarwa tsakanin 25 zuwa 27 ga watan Yuli a Luanda. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China