Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, jakadan ya tabbatar da cewa dukkan wasu bangarori na tauraron Angosat-1 na aiki kamar yadda aka tsara.
Ya kara da cewa, da Angosat-1, al'ummar kasar za su samu cin gajiyar fasahohin zamani da ake samu daga tauraron dan Adam, don samun tasoshin talabijin da karfin intanet domin samun ilimin fasahohi da kiwon lafiya daga wuri mai nisa da sauran alfanu.
Jakadan ya ce karuwar samun bayanai daga tauraron zai inganta ci gaban kasar musamman a bangaren masana'antu da harkokin banki da kuma tsaro. (Fa'iza Musatpha)