in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Faransa ya yi alkawarin sake gina majami'ar Notre Dame
2019-04-16 13:42:38 cri

A daren jiya Litinin, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana a wurin da gobara ta lalata majami'ar Notre Dame, cewar za a sake gina majami'ar wadda ta lalace sosai sakamakon gobarar.

Shugaba Macron ya kuma furta cewa, yana shirin kiran kafa asusun tattara kudi daga dukkanin sassan duniya, domin a sa hannu cikin aikin sake gina majami'ar Notre Dame baki daya.

Ban da wannan, Shugaban ya ce, bisa namijin kokarin da sassa daban daban na birnin Paris, musamman ma 'yan kwana-kwana guda dari biyar suka yi, an kashe wutar da ta tashi a hasumiyoyin kararawa guda biyu, da babban ginin, amma abin bakin ciki shi ne yawancin rufin ginin ya lalata, musamman ma yadda saman hasumiyar ya rushe.

A ranar 15 ga wata kuma, babban sakataren MDD António Guterres ya ba da labari ta shafin intanet na sada zumunta, cewar yana lura da gobarar da ta tashi a majami'ar Notre Dame. A cewarsa, majami'ar wani abin misali ne na musamman, na shahararrun kayayyakin tarihi na duniya, don haka zuciyarsa tana tare da gwamnatin Faransa da ma jama'arta a wannan lokacin.

Hukumar shari'a ta kasar Faransa ta kaddamar da bincike kan musabbabin abkuwar gobarar. Bisa rahotanni daga wasu kafofin watsa labarai, an ce, matsalar lantarki ce ta haifar da gobarar. (Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China