in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gobara ta tashi a majami'ar Notre Dame dake birnin Paris
2019-04-16 09:13:04 cri

A yammacin jiya Litinin gobara ta tashi a majami'ar Notre Dame dake birnin Paris na kasar Faransa, gobarar ta lalata babban dakin matuka, inda ta rushe hasummiyarsa. Kawo yanzu babu wanda ya rasa rai ko jin rauni a sanadin gobarar.

An ce, gobarar ta fara ne daga rufin dakin, daga baya kuma ta kara yaduwa cikin sauri zuwa sassan ginin. Masu kashe gobara a wurin sun bayyana cewa, mai yiwuwa gobarar ta tashi ne sakamakon aikin gyaran dakin da ake gudanarwa.

Ya zuwa karfe 9 na dare jiyan bisa agogon wurin, ba a samu nasarar kashe gobarar ba tukuna. Daruruwan mutane sun yi addu'o'i a kusa da majami'ar, kuma shugaban kasar Emmanuel Macron, da firayin ministan kasar Edouard Philippe, sun isa wurin cikin gaggawa. Shugaba Macron ya bayyana cewa, daukacin al'ummun kasarsa suna bakin ciki matuka da aukuwar gobarar da ta tashi a majami'ar Notre Dame.

Wannan rana kuma, shugabannin kasashen Birtaniya, da Jamus, da Amurka da sauransu su, sun mai da hankali kan wannan batun. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta bayyana a shafin sada zumuntar ta na yanar gizo cewa, gobarar da ta tashi a Notre Dame, ta sanya ta damuwa matuka, haka kuma ta sanya ta bakin ciki matuka, saboda Notre Dame alama ce ta al'adun Faransa, da ma al'adun kasashen Turai baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China