in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kara wa juna sani kan ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin a kasar Masar
2019-04-15 11:23:57 cri

An bude taron kara wa juna sani kan ilmin likitanci da maganin gargajiya na kasar Sin, Jiya Lahadi a birnin Alkahira, hedkwatar mulkin kasar Masar. Ma'aikatar kula da kiwon lafiya ta Masar, da cibiyar kula da lafiyar jiki ta Jami'ar ilmin zirga-zirga ta Shanghai, da ma Jami'ar Sin ta kasar Masar ne suka shirya taron tare.

Taron da zai shafe kwanaki biyu ana yinsa, na mai da hankali kan taken "raya ilmin likitanci da maganin gargajiya na kasar Sin, domin sa kaimi ga shirin kiwon lafiyar al'ummar duniya da ma cimma burin raya makomar bil adama ta bai daya".

A yayin taron kuma, kwararru da masana kan ilmin likitanci na Sin da Masar, za su tattauna kan yadda za a yada al'adun ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin, da ma makomar ilmin a yankin Gabas ta tsakiya da nahiyar Afirka, bisa aniyar kula da lafiyar al'ummar duniya da ma kara cudanyar kasashen biyu masu dogon tarihi.

Ban da wannan, an yi bikin kafa asibitin ilmin likitancin gargajiya ta Sin a kasar Masar a yayin taron.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China