in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban rikon kwarya na Sudan ya yi murabus
2019-04-13 16:32:59 cri

Gidan talibijin na kasar Sudan, ya ruwaito cewa, Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf, shugaban kwamitin mulkin soja na wucin gadi na kasar, ya sanar da yin murabus.

A daren jiya ne Ibn Auf, ya gabatar da jawabi ta gidan talabijin cewa, ya yi murabus daga mukaminsa domin kiyaye moriyar kasarsa, inda Laftana Janar Abdel Fattah Burhan zai maye gurbinsa.

A ranar Alhamis ne, Ibn Auf, ministan tsaron kasar na wancan lokaci, ya sanar da hambarar da gwamnatin dake karkashin shugabancin Omar al-Bashir. MDD da wasu kasashen duniya, ciki har da Rasha da Amurka da Turkiyya, da wasu kungiyoyin kasa da kasa, na fatan sassa daban daban na Sudan, za su kai zuciya nesa, tare da warware batutuwan dake ci musu tuwo a kwarya ta hanyar tattaunawa cikin ruwan sanyi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China