Kungiyar kwararru dake adawa da gwamnatin kasar, ta yi watsi da sanarwar da ministan tsaron kasar Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf ya yi.
Kungiyar ta jaddada cikin wata sanarwa cewa, za ta ci gaba da zaman dirshan har sai lokacin da aka mika mulki ga gwamnatin farar hula.
Ita ma kungiyar fafutukar 'yanci da sauyi ta The Freedom and Change Alliance, ta yi watsi da sanarwar da rundunar sojin ta fitar, ta na mai kira ga magoya bayanta da su ci gaba da zaman dirshan.
Haka zakalika ita ma Jam'iyyar adawa ta Sudanese Congress, ta yi biris da sanarwar ta rundunar sojin. (Fa'iza Mustapha)