in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta fitar da kudin tallafawa ayyukan agajin jin kai a Sudan
2019-04-12 10:45:59 cri
MDD ta fitar da dala miliyan 26.5 na bukatun gaggawa, domin bada tallafin ceton rayuka a kasar Sudan, cikin watanni 6 masu zuwa.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD, ya ce an fitar da kudin ne daga asusun agajin gaggawa na majalisar, domin samar da kayayyakin abinci da na kiwon lafiya da ruwa da na tsaftar muhalli ga mutane 800,000, wadanda karancin abinci da tabarbarewar tattalin arziki ya shafa a fadin jihohi 7 na kasar Sudan.

Sanarwar ta ce za a bayar da tallafin ne ga 'yan gudun hijira da al'ummomin da suka basu mafaka da kuma masu rauni.

Mataimakin Sakatare Janar na MDD kan ayyukan agaji, Mark Lowcock, ya ce matsalar tattalin arzikin ta shafi wasu fannoni da suka zarce rashin abinci.

Sanarwar ta kara da cewa, matsalar rashin abinci ta karu a Sudan, inda ake hasashen mutane miliyan 5.8 suka yi fama da yunwa tsakanin watan Junairun zuwa Maris na bana, adadin da ya karu sosai kan na shekarar 2018. Kuma mai yiwuwa ya kara karuwa daga watan Mayun kafin a fara samun amfanin gona.

Har wa yau, tallafin kudin zai bunkasa harkokin kiwon lafiya ga mutane 320,000 ciki har da yara da mata masu juna biyu, tare da samar da magungunan da kayayyakin aiki ga cibiyoyin lafiya 65 da horar da ma'aikatan lafiya ta masu bada agaji.

Baya ga haka, manoma da makiyaya dake yankunan da za a kai wa tallafin, suma za su samu tallafin kayyakin ayyukan gona da na kiwo da samun horo, domin inganta amfanin gona da na kiwo ga mutane sama da dubu 500. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China